Majalisar ministoci a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari ta amince da kafa kamfanonin casar shinkafa guda goma a jihohin Kebbi, Zamfara, Binuwai, Kogi da Bayelsa a kan Naira Bilyan 10.7.
Haka ma, majalisar ta amince da kashe Naira Bilyan 65.108 wajen kammala aikin hanyar Legas zuwa Ibadan.