Majalissar Ministoci Ta Amince Da Kammala Madatsun Ruwa Na Kano Da Jigawa


Majalisar ministoci a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari ta amince da kammala aikin Madatsun ruwan ruwan jihohin Kano da Jigawa wadanda aka yi watsi da su tun a shekarar 2000.

Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Albarkatun ruwa, ya ce, a halin, an kai kusan kashi 50 cikin 100 na aikin Madatsun ruwa wanda a cewarsa, idan aka kammala ayyukan za su bunkasa noman rani da kusan hekta 2000 inda ya kara da cewa ana sa ran kammala aikin a tsakanin watanni 24.

You may also like