Majalissar wakilan Najeriya zata dawo zama kan batun aringizon kasafin kudi. 


Majalisar Wakilan Najeriya zata dawo zama bayan hutun mako Takwas da duba batun Aringizo a kasafin Kudin Bana.
Sai dai babu mamaki Majalisar ta dauki mataki kan tsohon shugaban kasafin Kudi na Majalisar Abdulmumin Jibrin, wanda ya zargi shugabannin Majalisar da Aringizo a kasafin har ma yayi musu kiran da suyi murabus.

Tun fara takaddamar dai Majalisar ta tafi hutu da ake ganin da zarar ta dawo zama Talatar nan zata fara tattaunawa ne kan lamuran Aringizon.

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya EFCC ta fara binciken zargin, wannan takaddama dai ta kawo ra’yoyin mabanbanta tsakanin masu ganin ‘yan Majalisar na da zargin da zasu amsa da kuma masu ganin sunyi aiki ne bisa ka’idarsu ta dokar aikin Majalisa.

Abin tambaya anan shine ko ‘yan Majalisar zasu amsa wannan kira, a zahiri dai babu bangaren da ya sassauta. An rawaito dai shugaban kwamitin Labarun Majalisar Wakilan Abdulrazak Namdas, na cewa Majalisar zata dau matakai ne bisa doka, don haka sai a jira zaman Majalisar don ganin irin matakin da za a dauka.

You may also like