Majalissun Najeriya zasu gana da Buhari kan tattalin arziki. 


Shugaban majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya kira taron Majalisun kasar don yi musu bayani kan matsalar tattalin arzikin da ta addabi kasar.
Yayin da yake jawabi a zauren Majalisar, Dogara ya ce yana da matukar muhimmanci shugaban kasar ya yi wa ‘yan Majaisu da al’ummar Najeriya bayani kan halin da ake ciki da kuma irin matakan da yake dauka.

An dade ana rade-radin cewar shugaban zai bukaci Majalisun sun ba shi damar kafa dokar ta baci don ceto tattalin arzikin kasar.

You may also like