Majalisun Tarayya Zasu Kashe Zunzurutun Kudi Har Naira Biliyan 6 Wajen Siyan Motoci Majalisun tarayya sun bayyana yadda suke kashe kasafin kudinsu bayan da suka shafe Shekaru 8,suna boye yadda suke kashe kudaden da suka ware a kasafin kudinsu.

Gabaki dayan kasafin kudin da majalisar ta ware a wannan shekarar ya kama naira biliyan 125, karin naira biliyan 10 kan kudin da ta kashe a shekarar data gabata.

Yayin da majalisar dattijai ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 2 da miliyan dari 6 domin siyan motoci,  ita kuwa takwararta ta wakilai ta ware naira biliyan 3 da miliyan dari 8 domin sayan nata motocin.

You may also like