Makarantar Horar da Sojoji na musamman ta koma Buni Yadi


000_Par8254355(1)_0

 

Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da cibiyar horar da sojoji na musamman zuwa garin Buni Yadi na Jihar Yobe, wanda Mayakan Boko haram suka taba kwacewa.

An dauke makarantar ne daga Jihar Niger kuma babban hafsan sojin Kasar Janar Tukur Buratai ya ce saboda fada da Boko Haram aka dawo da makarantar zuwa Buni Yadi.

Janar Buratai ya ce Buni Yadi ya kasance hanyar da mayakan na Boko Haram ke bi zuwa sassan yankin arewa maso gabashi har zuwa Jihar Filato.

An kirkiro Makarantar ne ta horon sojoji na musamman a lokacin da sojojin Najeriya ke fada gadan-gadan da Mayakan Boko Haram

You may also like