Makarantun Da ‘Ya’Yan Shugaba Buhari Suka Yi Da Shekarun Haihuwarsu


Jaridar Premium Times ta wallafa wani sashe na littafin da wani farfesa a kasar Amurka, John Paden ya rubuta akan shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna ‘Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria’ inda suka zayyano makarantun da ‘yayan shugaban kasar suka yi daya bayan daya da shekarun da aka haife su.

Ga fassarar wallafar:

1. Fatima: An haifi Fatima ranar 7 ga watan Maris, 1975. Ta yi makarantar firamari dinta a firamarin Sojojin Sama da ke Victoria Islands a jahar Lagos, ta yi karatun sakandaren ta a Kwalejin gwamnati dake Kaduna wato Government College, Kaduna; sannan ta yi digirin ta na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria kafin ta tafi kasar Ingila domin yin karatun babban digiri dinta a harkar kasuwanci.

2. Nana-Hadiza: An haifi Nana Hadiza a ranar 23 ga watan Yuni 1981. Ta fara karatunta ne a Makarantar Essence International School da ke Kaduna sannan ta tafi Kasar Ingila domin Cigaba da karatunta.

Ta yi Karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Buckingham duk a kasar Ingila sannan ta dawo Kaduna domin yin babban digirinta a fannin Malanta a ‘National Teachers Institute’ da ke Kaduna. Ta yi digirin mastas dinta a Kwalejin Kimiyya da fasaha da ke Kaduna (Kaduna Polytechnic).

3. Safinatu: An haifi Safinatu ranar 13 ga watan Oktoba 1983. Ta yi karatu a makarantar Essence International School sannan ta wuce kasar Ingila domin yin karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Plymouth, duk a kasar ingila sannan har yanzu tana karatu a Jami’ar Arden da ke kasar can.

4) Halima: An haifi Halima ranar 8 ga watan Oktoba 1990. Tayi Makarantar Essence International School, sannan ta ci gaba a makarantar British School of Lome; Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Leicester duk a kasar Ingila. Daga nan ta dawo makarantar koyan aikin lauya a Nijeriya.

5) Yusuf: An haifi Yusuf a ranar 23 ga watan Afrilu. Ya yi karatunsa ne a Kaduna International School; British School of Lome; Kwalejin Bellerby’s da Jami’ar Surrey, duk a kasar Ingila.

6) Zahra: An haifi Zahra ne ranar 18 ga watan Disemba 1994. Ta yi karatunta a makarantar Kaduna International School; British School of Lome; Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Surrey duk da ke kasar Ingila.

7) A’isha (Hanan): An haifi A’isha ranar 30 ga watan Agusta 1998. Ta na karatunta a makarantar Kaduna International School.

8) Noor (Amina): An haifi Noor ranar 14 ga watan Satumba 2004. Ta na karatun ta a Kaduna International School.

Babbar ‘yar Buhari mai suna Zulaihat ta rasu a shekara ta 2012 a dalilin ciwon ‘sickle cell anemia’ a yayin nakuda. Kafin nan iyalin Buhari sun rasa yaro namiji mai suna Musa, a lokacin da ya na jariri shi ma a sakamakon ciwon na’sickle cell anemia’

You may also like