Sarkin Katsina, Alhaji Kabir Usman ya bayyana cewa makiyan Shugaba Buhari ne ke daukar nauyin rikice rikicen da ake fama da su a duk fadin kasar nan don ganin sun shafa masa bakin jini a idon magoya bayansa.
Sarkin ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar tsohon Gwamnan Katsina, Marigayi Lawal Kaita inda Sarkin ya nuna cewa manufar haddasa rikice rikicen shi ne na Ingiza al’ummar Nijeriya kan yi gwamnatin Buhari bore don ganin sun gurgunta kokarin d yake yi na farfado da martabar kasar nan.