Makiyaya Sama Da 50 Sun Mutu A Wani Harin Jirgin Sama A Jihar NasarawaPLATEAU, NIGERIA – Harin jirgin saman a kan iyakar jihohin Nasarawa da Binuwai ya hallaka rayukan gwamman makiyaya a kauyen Rukubi dake Jihar Nasarawa.

Taron Fulani Makiyaya

Taron Fulani Makiyaya

Ardon Ardodin Jihar Nasarawa, Lawal Dono wanda shine kuma shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a Jihar Nasarawa ya ce jirgin ya kashe mutane fiye da hamsin.

To sai dai har lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa bata ce kome kan lamarin ba, duk da kira da muka yi wa kakakinta, DSP, Ramhan Nansel.

Shanun Fulani Makiyaya

Shanun Fulani Makiyaya

A bangaren gwamnati kuwa, mai ba gwamnan Jihar Nasarawa shawara kan harkokin makiyaya da manoma, Abubakar Ladan ya ce gwamnati na daukar matakan kawo karshen wadannan kashe-kashe.

Matsalar tsaro a kan iyakar Jihohin Nasarawa da Binuwai dai na da tsohon tarihi kuma ba wannan ne karo na farko da jirgi ke luguden wuta kan jama’a a yankin ba, don ko a shekarar bara, wani jirgi ya hallaka mutane da dama a yankin.

Saurari cikakken rahoton daga Zainab Babaji:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like