Makomar Afirka a sabuwar gwamnatin Amirka


 

 

Donald Trump ya na ganin nahiyar tamkar matattara ce ta shugabanni marasa adalci da wadanda suka yi fice wajen cin hanci da salon mulki irin na “Sai Mahdi ka Ture”.

Tuni dai Donald Trump ya yi barazanar jefa shugabanni irin su Robert Mugabe na Zimbabuwe da Yoweri Museveni na Yuganda a gidan kaso. Sabon shugaban Amirkan dai ya kasance mai kaunar Nelson Mandela, sai dai yakan bayyana kasar Afirka ta Kudu a matsayin aljannar miyagun ayyuka.

To sai dai ba Trump kadai ba, shi ma Barack Obama nahiyar Afirka ba ta cikin wuraren fifikon gwamnatinsa. Kamar yadda masanin kimiyyar siyasa na kasar Kenya Barrack Muluka ya bayyana:

“Ba na tunanin Afirka na da wani tasiri ta kowane siga a cikin manufofin ketare na Amirka, musamman idan sabon Shugaba Donald Trump ya karbi ragamar mulki daga Barack Obama”.

To sai dai ga kasashen na Afirka, Amirka muhimmiyar abokiyar hulda ce a garesu, musamman a bangaren bada taimakon raya kasa, a daya hannun kuma na biyu a fannin zuba jari.

Tansania US Wahlen PR Aktion (Getty Images/AFP/D. Hayduk)Wasu ‘yan Afirka a Amirka murna ta koma ciki

Dangantakar kasuwanci tsakanin Amirka da kasashen Afirka da ke Kudu da Sahara ya dara kasafin kudin Amirkan, balle a samu hadin kai wajen ayyukan raya ci gaba. bayan Turai da China, Amirka ta kasance ta uku a huldar kasuwanci da Afirka. Sai dai Trump na muradin yarjejeniyar kasuwanci ne da Amirka za ta ci moriya, a cewar mai magana da yawun gwamnatin Habasha Negeri Lencho. Masu lura da al’amura na fargabar cewar, yarjejeniyar inganta kasuwancin Afirka da ba wa nahiyar damarmaki da aka amince da ita a shekara ta 2000, za ta shiga cikin halin ni ‘yasu, wato yarjejeniyar ba su damar shigar da hajarsu zuwa Amirka ba tare da biyan haraji ba.

Sai dai masanin tattalin arziki da halayyar dan Adam a nan Jamus Robert Kappel, baya ganin akwai wani gagarumin sauyi da za a samu a kasancewar Afirka ba ta da wani muhimmanci ga Amirka a fannin kasuwanci.

Kamerun US-Botschafterin Samantha Power in Mokolo (picture alliance/AP Photo/A. Harnik)Amirka kan sa baki a harkokin tsaron Afirka

Boko Haram a yankin Yammacin Afirka, masu tsattsauran ra’ayin addini a Sahel da Al-Shabaab da ‘yan fashin jiragen ruwa a Somaliya, ga Amirka dai amfani da ayyukan ta’ada a Afirka na bangaren matakin yakar ta’addanci da duniya da aka dade a ciki. Ko shakka babu, Amirka za ta rage ayyukan sojinta a Afirka a karkashin gwamnatin Trump, a cewar Stephen Chan, Farfesa a cibiyar nazarin lamuran Amirka da ke London.

” A kasashen Afirka da ke Kudu da Sahara, babu abun da zai sauya dangane da masu tsatstsauran ra’ayi, domin wannan ba damuwan Amurka ba ce, Donald Trump ba shi da wani tsari takamamme da ya danganci Afirka”.

Wasu ayyukan raya kasa kamar shirin “Power Africa” wanda Barack Obama ta kirkira zai rushe, da ke da nufin ba wa mutane miliyan 60 wutar lantarki.

You may also like