
Asalin hoton, AP
Dan wasan tsakiya na Scotland mai taka leda a Manchester United, Scott McTominay, mai shekara 26, ka iya komawa Bayern Munich , idan kungiyar ta gagara dauko dan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, daga kungiyar Fulham a watan Junairun badi. (Mirror)
Zai zama abin mamaki idan Chelsea idan ta saida dan wasa Reece James da Real Madrid tke zuba wa ido, ian kwantiragin dan wasan baya na Ingilar mai shekara 23 a shekarar 2028. (Football Insider)
Aston Villa ta bi takwarorinta na Liverpool da Barcelona ia zawarcin dan wasan Sifaniya, mai taka leda a Athletic Bilbao, Nico Williams, mai shekara 21idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar nan. (Diario AS – in Spanish)
Brighton za ta sake sabon lale, kan dan wasan baya na Argentine, Valentin Barco, mai shekara 19, kafin bude kasuwar saye da saida ‘yan wasa a watan Junairu(Sun)
West Ham da Crystal Palace ka iya sabunta aniyarsu ta daukar dan wasan baya na Faransa, mai taka leda a Paris St-Germain’s Hugo Ekitike, mai shekara 21, a watan Junairu. (Football Insider)
Ana sa ran dan wasan Italiya Ciro Immobile, mai shekara 33, zai ci gaba da zama a kungiyar Lazio, duk da zawarcinsa da kungiyoyin Saudiyya wato Al-Shabab da Al-Wehda, ke yi. (Corriere dello Sport – in Italian)
Tsohon kocin Jamus Joachim Low na sahun gaba cikin wadanda ake fatan zabar daya da zai maye gurbin koci Stefan Kuntz a matsayin mai horas da ‘yan kwallon Turkiyya. (DHA – in Turkish)
Hukumar kwallon kafar Turkiyya ta fara tattaunawa da tsohon tsohon dan wasan gaba na Italiya, Vincenzo Montella, da ya kawo karshen zaman tsohon koci Kuntz a kungiyar Adana Demirspor a watan Yuli. (Nicolo Schira)