
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa zuwa Yunin 2023, za ta daina biyan kuɗin tallafin fetur da ta saba biya.
Ministar kuɗi da kasafi ta ƙasar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke gabatar da kasafin na 2023 ga jama’ar ƙasar.
Ta bayyana cewa a 2023, gwamnatin ta ware naira tiriliyan 3.36 ne kawai domin biyan tallafin fetur na wata shidan farko na shekarar.
Ta kuma ce wannan matakin na tafiya ne da ƙarin wa’adi na watanni 18 na cire tallafin da aka sanar a 2022.
A lokacin da take bayani kan gundarin kasafin, ministar ta bayyana cewa kuɗin shigar da ƙasar ke samu zuwa Nuwambar 2022 ya kama tiriliyan 6.5, wanda hakan ke nufin ya kusa kai adadin da ƙasar ke da burin samu a bana na tiriliyan 7.8
Ministar kuma ta bayyana ɗaya daga cikin masu kawo wa ƙasar kuɗin shiga akwai naira biliyan 586 wanda ita da kanta gwamnatin tarayya ke samarwa sai kuma hukumar kwastam ta ƙasar mai kawo naira biliyan 15.
Haka kuma akwai harajin da ake karɓa daga jama’a wanda ya kai tiriliyan 1.3 da kuma tiriliyan 3.7 da ake karɓa daga sauran ɓangarori.
Manyan ɓangarorin da suka tallafa wa tattalin arziƙin ƙasar a 2022 akwai ɓangaren noma wanda ya samar da kashi 23 cikin 100 da kuma ɓangaren sadarwa da kasuwanci da man fetur da suka bayar da kashi 5.6.
Raguwar da ake samu na tallafin da fetur ke bai wa ƙasar ya sa gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar samun hanyoyin kuɗin shiga ga ƙasar.
Sai dai a halin yanzu, gwamnatin Shugaba Buhari za ta miƙa mulki ga sabuwar gwamnati a Mayun 2023 bayan zaɓen da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Babbar tambayar a nan ita ce mece ce matsayar waɗanda suke takarar shugabancin Najeriyar a game da tallafin man fetur?
Atiku Abubakar
Asalin hoton, Getty Images
Atiku Abubakar wanda shi ne ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar PDP ya bayyana cewa zai cire tallafin man fetur sa’annan kuma ya karkatar da kuɗin ta ɓangaren sufuri da kuma ilimi.
“Duk wasu kuɗi da muke samu muna ɗaukar su domin biyan bashi. Idan da za mu ɗauki matakai masu kyau, za mu iya samun kuɗi masu yawa da za su taimaka a yi manyan ayyuka da biyan albashi da na gudanarwa,” in ji Daniel Bwala, mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku kamar yadda ya shaida wa wata kafar watsa labarai ta Najeriya.
Atiku ya bayyana cewa tallafin fetur shi ke lashe kashi 60 cikin 100 na bashin da Najeriya ke biya a duk shekara.
“Za mu iya samun kuɗi masu yawa domin zuba jari a ɓangaren wuta da man fetur da ilimi idan muka cire tallafi,” in ji shi.
Bola Tinubu
Ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu shi ma ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan batun cire tallafin man fetur.
Tinubu ya bayyana cewa kowace irin zanga-zanga jama’a za su yi, ba zai jingine aniyarsa ta cire tallafin fetur din ba.
“Ta ya za a biya tallafin man fetur ɗin da ake sha a Kamaru da Nijar da Jamhuriyyar Benin. Duk irin zanga-zangar da za ku yi, sai mun cire tallafin man fetur,” in ji shi.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC ya ce gwamnatinsa za ta bayar da dama ga kamfanoni masu zaman kansu su wataya ba tare da saka musu ido ba inda ya ce hasali ma zai taimaka musu ne.
Peter Obi
Shi ma ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar LP Peter Obi ya caccaki tsarin Najeriya na biyan tallafin man fetur.
Peter Obi ya sanar da cewa ya yanke shawarar kawo ƙarshen wannan matakin ta hanyar tura kuɗaɗen ta ɓangaren wutar lantarki da kiwon lafiya da ilimi idan aka zabe shi a 2023.
Ya kuma ƙara da cewa irin adadin kuɗin da aka kashe kan tallafin man fetur a shekara 12 da suka wuce ya isa ya magance matsalolin da ake da su a ƙasar da suka haɗa da na ilimi da kiwon lafiya da ɓangaren lantarki.