Makudan kudin yaki da ta′addanci | Labarai | DWBurin da fadar mulki ta Niamey ke son cimma wa da kudin shi ne na karfafa dakarun tsaro ta fannoni da dama, ciki har da kwarin gwiwar jajircewa a fagen daga da kare fararen hula.

Ita dai kungiyar ta EU da ke dasawa da Nijar, ta ce za ta gina wani sansanin soja a yankin Tillaberi da ke yammacin kasar, da kuma kafa wata cibiyar horas da jami’an tsaro makamar aiki.

Jamhuriyar Nijhar ta zama kasar da Faransa ta dogara a kanta a yankin Sahel, tun bayan da Mali ta bukaci sojanta su kwashe nasu-ya-nasu su fice daga kasar bayan shafe fiye da shekaru tara suna yaki da ta’addanci.You may also like