Malaman Izala Sun Fara Tattauna Batun Kisan Sheikh Jafar Majalisar Malaman Izala sun yi taron manema labarai dangane da batun zargin kisan kan da aka yi wa Sheikh Jafar. Haka kuma majalisar ta baiwa hukumar tsaro wa’adin mako biyu domin fitar da bayanin da aka ce an sami takardar dake nuna hannun tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau a kisan.

You may also like