Malamar da girgizar ƙasa ta hallaka duk ɗalibanta a Moroko



School bags and a chair in a school

Asalin hoton, Adaseel Schools

  • Marubuci, Yassmin Farag
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

“Na shiga tunanin ina riƙe da rijistar ɗalibai ina jan layi kan sunan ɗalibai ɗaya bayan ɗaya, har sai da na goge sunaye 32; waɗanda duk sun mutu.”

Nesreen Abu ElFadel,malamar da ke koyar da darasin Arabiya da Faransanci a Marrakesh, tana tuna yadda ta ruga zuwa ƙauyen Adaseel da ke kan tsauni a Morocco, tana ƙoƙarin tono ɗalibanta daga ɓaraguzai bayan giegizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.8 da ta afka wa ƙasar.

Nesreen da mahaifiyarta a kan titi suke barci bayan girgizar ƙasar ta ranar Juma’a.

Bayan ta ji labarin girman ɓarnar da girgizar ƙasar ta yi wa ƙauyen, nan take ta fara tunanin makarantar da take koyarwa – makarantar Adaseel da kuma ɗalibanta waɗanda take kira ‘ya’yanta.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like