Malamin coci: Ni dan luwadi ne


 

 

 

Wani malamin coci na kasar Ingila ya shaida wa duniya cewa shi dan luwadi ne kuma yana alfaharin da kasancewar sa haka..

A ranar Asabar din nan ne ,malamin garin Grantham Nicholas Chamberlain ya bayyana kansa a yayin wata tattaunawar da ya yi da manema labarai na Jaridar Birtaniya The Guardian.

Chamberlain ya ce, ya yi hakan ne domin taushe bakin wani mutum da ya yi  barzanar tona asirinsa.

Malamin ya ci gaba da cewa,bai bayyana kansa domin haifar da cece-kuce ba.Domin mafi yawa daga cikin wadanda ke zuwa cocinsu salla sun jima da sanin shi dan luwadi ne.Haka zalika,cocin da ta nada shi a matsayin wanda zai dinka ma jama’a wa’azi ma ta san da hakan

You may also like