Mallorca ta ci Real Madrid a wasan La Liga ranar Lahadi



Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Mallorca a La Liga ranar Lahadi, inda Marco Asensio ya barar da fenariti

Tun a minti na 13 da fara wasa Real ta ci gida ta hannun mai tsaron bayanta Nacho Fernandez a Estadi Mallorca Son Moix.

A minti na 59 aka bai wa Real bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da gola, Predrag Rajkovic ya yi wa Vinicius Junior. keta.

To sai dai kuma Rajkovic ya tare kwallon da Asensio ya buga masa ta bangaren hagu.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like