Matashin mai suna Kweku Mensah ya rataye kansa ne saboda sun yi hatsaniya da budurwar sa inda ta shaida masa cewa zata yanke alaka dashi marigayin.
Al’amarin Ya faru ne a wani gari mai suna Axim dake arewacin kasar Ghana. Shugaban matasan yankin Axim Mista Kofi Nokoe ya shaidawa ma nema labarai cewa sun tsinci gawar mista kweku ne a rataye a jikin bishiya, inda daga nan suka rankaya da gawar zuwa asibitin yankin na Axim.