Mamaki: Maza Da Mata Na Gudanar Da Ibada Waje Daya A Cikin MasallaciMasallacin mai  suna Ibn Rushd-Goethe yana gine ne jikin wani cocin Protestant da ke birnin Berlin. Masallacin na wasu  mutane ne da suka kira kansu masu sassaukan ra’ayi  akan Addini a Kasar Jamus inda mata da maza ke taruwa sahu Daya suna sallah a tare. Wannan masallaci shi ne irinsa na farko a kasar ta Jamus. 

A wannan masallaci, ‘yan Sunni da ‘yan Shi’a na yin ibada a tare kuma an sahalewa mata da su shiga masallacin tare da aiwatar da duk nau’in ibadar da suka yi niyya ba tare da sanya hijabi, mayafi ko kallabi ba. 

Wata mai kare ‘yancin mata, Seyran Ates, ta bayyana cewa sun shafe shekaru kusan takwas suna fafuttukar nemawa musulmai irin wannan wajen bauta amma abin ya gaggara sai a wannan karon Seyran Ates, ta bayyana cewa  “Rashin hadin kai a wuraren bauta ne ke haddasa yawaitar ta’addanci da munanan ayyuka a addinin musulunci wanda kamata ya yi a ce mu musulman zamani mu hada kan mu awuraren bautarmu.

You may also like