Mamakon Ruwan Sama Yayi Awon Gaba Da Wata Gada A jihar Neja 


Mallakar Hoto:Daily Trust

Ambaliyar ruwa bayan mamakon ruwan sama  tayi awon gaba da wata gada da ta hada yankin kudu maso yamma da kuma yankin arewa maso yammacin kasar nan,ta bangaren Jebba/Mokwa da kuma Kontagora a jihar Neja. 

Titin da gadar ta karye na daga cikin titunan gwamnatin tarayya dake hada jihar ta Neja da sauran bangarorin kasarnan.

Wakilin jaridar Daily Trust ya rawaito cewa  manyan motoci uku ne da kuma karama guda daya ruwan yayi awon gaba dasu.

 Mazauna yankin sun ce gadar ta dade cikin wani hali dake bukatar kulawa, ta kuma karye ne a ranar lahadi da misalin 9 na dare sakamakon ruwan sama mai yawan gaske, wanda yakai har ranar Litinin anayi. 

Karyewar gadar ya jawo jerin gwanon motoci ta kowanne bangare da suka fito daga yankin kudu maso yamma da yankin arewa maso yamma. 

 Kwamishinan aiyuka da sufuri na jihar Neja Mallam Abdulmalik cheche, da takwaransa  na yada labarai Jonathan Vatsa,suka kai ziyarar gani da ido wurin.

Vatsa, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta tura ma’aikata domin gyaran gadar.

You may also like