Mamaye Burtaloli Ke Janyo Rikicin Fulani Da Manoma – Ministan Tsaro


Ministan Harkokin tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan Ali ya alakanta rikice rikicen makiyaya da manoma da ake fama da su a jihohin Binuwai da Taraba a kan yadda mutane suka mamaye Burtulolin da Shanu ke bi.

Ministan ya yi wannan ikirarin ne bayan wani taro da ya yi da shugabannin rundunonin tsaron kasar nan a Fadar Shugaban kasa inda ya jaddada cewa gwamnati ta yi alwashin kawo karshen wadannan rikice rikicen.

You may also like