Mambobin gwamnatin kasar Malaysia sun amince da rage albashinsu da kaso 10


Firaministan kasar Malaysia, Mahathir Mohamad ya sanar da rage albashin ministocinsa da kaso goma cikin dari.

Rage kudin albashin wani bangare ne na kokarin da gwamnatinsa ke yi na rage kashe kudade domin ta samu ta yi maganin dimbin bashin da ake bin kasar da yawansa ya kai dalar Amurika biliyan $250.

Mahathir, wanda shine shugaban kasa mafi tsufa da aka zaba a duniya ya bayyana haka a wurin taron majalisar zartarwarsa da ministoci sama da sha biyu suka halarta.

“Mun damu akan matsalar kudade da kasar mu ke fama da ita,”Mahathir ya fadawa manema labarai bayan taron.

Mahathir ya ce ba zai takura sauran ma’aikatan gwamnati ba su dauki irin wannan mataki amma za su iya yin haka idan suna so su bada gudummawarsu wajen rage kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like