Mambobin jam’iyar APC 800 sun sauya sheka ya zuwa PDP a jihar Kwara


Mallakar Hoto:Jaridar Daily Trust

Mambobin jam’iyar APC da ba su gaza 800 ba ne suka sauya sheka ya zuwa jam’iyar adawa ta PDP a jihar kwara.

Iyiola Oyedepo, shugaban jam’iyar na jihar shine ya karbi mutanen ranar Juma’a a Ilorin lokacin da shugabannin jam’iyar na Shiyar Arewa Ta Tsakiya suka ziyarci jihar.

Dakta Hanafi Alabare, wanda ya jagoranci masu sauyar shekar daga mazabar Alanamu dake karamar hukumar Ilorin ta Yamma ya ce  sun gaji da jam’iyar APC.

Oyedepo a nasa jawabin ya shedawa shugabannin shiyar cewa tun shekarar 2015 manyan mambobin jam’iyar ta APC ke ficewa daga jam’iyar.

Ya bayyana sauya shekar Alabare da kuma mutanensa a matsayin wata alama dake nuna farin jinin jam’iyar  PDP a jihar.

Shugaban shiya na jam’iyar Mista Theophilus Daka ya yabawa shugabannin jam’iyar na jihar kan yadda suka rike jam’iyar gida guda duk da rikicin cikin gida da take fama da shi.

You may also like