
Asalin hoton, EPA
Makwabtan juna Manchester United da Manchester City sun kai zagayen kusa da na kusa da ƙarshe ko kuma kwata fayinal a kofin kalubale na Carabao.
City ta doke Liverpool a Etihad 3-2, ta hannun Erling Haaland da Riyad Mahrez da kuma Nathan Ake.
Ita kuma United ta doke Burnley ne 2-0.
A yanzu City za ta kara da Southampton wadda ta cinye Lincoln City, yayin da Man United za ta kara da Charlton Athletic.
A ranar 26 ne za a dawo gasar Premier League bayan shafe makonni ana hutun gasar Kofin Duniya da aka kammala a Qatar.
Anan ma, Manchester United za ta kwashi ‘yan kallo ne da Nottingham Forest, City kuma da Leeds United.