
Asalin hoton, OTHER
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce zamansa a kungiyar ba zai zama mai cikakkar nasara ba matsawar ba su lashe kofin zakarun Turai ba.
Guardiola ya tsawaita zamansa City ne zuwa 2025, yayin da ake hutun gasar kofin duniya.
Kungiyar ta Etihad ta lashe manyan kofuna tara tun bayan zuwan kocin a 2016.
To amma har yanzu ba su yi nasarar lashe kofin zakarun Turai ba.
A 2021 ne ma suka so lashe kofin, a wasan da Chelsea ta yi nasara kansu a wasan karshe.
”Ba kofin zakarun Turai ne ba kawai kofi, amma zan fadi cewa shi ne kofin da muke bukata, kuma zamana a kungiyar ba zai kammalu ba idan bamu ci shi ba.” In ji Guardiola.
Ya kara da cewa ‘ Ina ji a jikina yan wasanmu za su ci shi nan kusa.”
City za ta kara da RB Leipzig a zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai.
Kuma a bana tana kokarin kafa tarihin zama kungiya ta biyar da ta taba cin kofin Premier sau uku a jere.
A ranar Alhamis za ta buga da Liverpool, a zagaye na hudu na kofin Carabao.
Sai dai City na da yan wasan da yanzu suke dawowa atisaye, saboda halartar gasar kofin duniya da suka yi a Qatar.