Man City na gaban Real Madrid a zawarcin Bellingham, Liverpool za ta yi cefane mai yawaJude Bellingham

Asalin hoton, LEE SMITH/REUTERS

Bayanan hoto,

Tun a makarantar firamare Jude Bellingham ya yi fice

Manchester City na gaban Real Madrid a zawarcin Jude Bellingham na Borussia Dortmund bayan da Liverpool ta hakura da sayen matashin dan wasan na Ingila mai shekara 19. (ESPN)

Dan wasan West Ham na Ingila Declan Rice, da na Brighton mai shekara 21 dan Ecuador Moises Caicedo da na Inter Milan dan Italiya Nicolo Barella da dan Wolves na Portugal Matheus Nunes, har yanzu suna cikin jerin ‘yan wasan tsakiya da Liverpool ke zawarci. (Florian Plettenberg)

Barcelona za ta kara tashi tsaye a zawarcin da take yi na Ilkay Gundogan sakamakon irin kokarin da dan wasan na tsakiya na Jamus ya yi a karawar da Manchester City ta doke Bayern Munich a gasar Zakarun Turai. (Sport)

Arsenal da Liverpool da kuma Manchester United na sa ido a kan matashin dan wasan tsakiya na Bayern Munich Ryan Gravenberch dan Netherlands (Footmercato)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like