
Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na zawarcin dan wasan Chelsea da Ingila, Ben Chilwell, 26 a bazara. (CaughtOffside)
Chelsea ta bayyana ɗan wasan Napoli kuma ɗan Najeriya, Victor Osimhen, 24, a matsayin na gaba-gaba a waɗanda take zawarcinsu a kaka ta gaba. (90min)
Tottenham ta nuna sha’awar sayen ɗan wasan Crystal Palace mai buga wa Ingila, Marc Guehi, 22, yayin da suke neman sayen masu tsaron gida biyu a kaka mai zuwa. (Mail)
Ɗan wasan Barcelona mai buga wa Ivory Coast tsakiya Franck Kessie, 26, ya ƙi amincewa ya koma Tottenham a kasuwar musayar ƴan wasa a January. (Sport – in Spanish)
Inter Milan ta shirya ta ƙara tattaunawa da Chelsea kan ƙulla yarjejeniyar din-din-din da ɗan wasan gaba na Belgium Romelu Lukaku. A yanzu ɗan wasan mai shekara 29 yana a matsayin aro a Serie A. (Gazzetta dello Sport – in Italian)
Ajax na ƙara ƙaimi a ƙoƙarin neman daraktan wasanni na Liverpool Julian Ward idan ya ajiye muƙaminsa a Anfield a karshen kakar wasa ta bana. (Telegraph – subscription required)
Leeds na zawarcin kocin Feyenoord Arne Slot ya zama manajansu. (Times – subscription required)
Barcelona na son tsawaita kwantiragin kyaptin ɗin kulob ɗin kuma tsohon ɗan wasan Spaniya Sergio Busquets, 34. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Liverpool na ci gaba da zawarcin ɗan wasan Birmingham City George Hall. Everton da Leeds na son sayen ɗan wasan tsakiyar mai shekara 18. (Football Insider)
Barcelona za ta nemi ɗan wasan baya na Bayern Munich da Faransa, Benjamin Pavard, 26, a bazara. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti na iya shirin maye Tite a matsayin kocin Brazil. (GeGlobo, via DefensaCentral – in Spanish)