Man City ta dauki Maximo Perrone wanda za ta mora nan gaba



Maximo Perrone

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta dauki dan kwallon Argentina, Maximo Perrone kan yarjejeniyar kaka biyar da rabi kan fam miliyan takwas daga Velez Sarsfield.

Mai shekara 20 mai buga wasa daga tsakiya ya ci kwallo uku a karawa 33 da ya yiwa Velez, wadda ya fara yi mata tamaula a Maris din 2020.

Ya taimaka da kungiyar da ke birinin Buenos Aires ta kai daf da karshe a bara a Copa Libertadores,, sai dai bai yi karawar da Flamengo ta doke su ba.

Perrone yana yi wa tawagar Argentina ta matasa ‘yan kasa da shekara 20 tamaula.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like