Man City ta kammala daukar Leroy Sane


Manchester City ta kammala daukar Leroy Sane daga kungiyar Schalke a kan kudi fan miliyan 37.

Sane, mai shekara 20, ya sanya hannu a kan yarjejeniyar shekara biyar.

Dan wasan ya buga wa tawagar kwallon kafar Jamus tamaula a gasar cin kofin zakarun Turai da aka yi a Faransa a cikin watan Yuli.

Sane ya ci wa Schalke kwallaye takwas daga wasanni 33 da ya buga a gasar Bundesliga ta Jamus.

You may also like