
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea na daf da ɗauko ɗan wasan gaba na Ivory Coast David Datro Fofana, mai shekara 19, daga kulob ɗin Molde na ƙasar Norway a kan kuɗi sama da yuro miliyan goma.
Arsenal na cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama da suka shiga tattaunawa don cimma yarjejeniya da ɗan wasan gefe na Ukraine Mykhaylo Mudryk amma Shakhtar Donetsk ta dage cewa shugaban kulob ɗin ne zai yanke shawara kan makomar ɗan wasan mai shekara 21, da zarar sun samu kowanne irin tayi a hukumance.
Liverpool za ta lale kuɗi har yuro miliyan 150 kan ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund na ƙasar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, da kuma wata yuro kimanin miliyan 100 don sayen ɗan wasan tsakiya na Benfica haifaffen Argentina, Enzo Fernandez, mai shekara 21.
A lokaci guda kuma, shirin Manchester City na sayo sabbin ‘yan wasa ya fi karkata a kan Bellingham da kuma ɗan wasan gefen Arsenal haifaffen Ingila Bukayo Saka, mai shekara 21.
Kamfanin ejan ɗin da ke wakiltar ɗan wasan tsakiyar Fiorentina Sofyan Amrabat, mai shekara 26, na son ɗan ƙwallon duniyar na ƙasar Moroko ya shiga Liverpool.
Ɗan wasan gaban Portugal da ke buga wa Atletico Madrid Joao Felix, mai shekara 23, wanda aka gabatar da shi ga ƙungiyoyin Firimiya Lig irinsu Arsenal da Manchester United, ya fi son zuwa Paris St-Germain don ci gaba da buga ƙwallo.
Ɗan wasan gaban Jamus Youssoufa Moukoko, mai shekara 18, na daf da sa hannu kan wata sabuwar kwanturagi da Borussia Dortmund duk da sha’awar da Chelsea, da Manchester United da kuma Liverpool suka nuna a kansa.
Manchester United da Newcastle na rige-rige da Real Madrid kan ɗan wasan gefe na PSV Eindhoven na ƙasar Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 23.
Sai Wolves ta yi da gaske wajen korar kulob da yawa na Firimiya Lig waɗanda su ma ke son ɗaukar ɗan wasan gaban Atletico Madrid kuma ɗan ƙasar Brazil Matheus Cunha, mai shekara 23.
Chelsea za ta “sake jarraba sa’a” a ƙoƙarinta na ɗauko ɗan wasan gaban AC Milan na ƙasar Portugal Rafael Leao, ma shekara 23, daidai lokacin da koci Graham Potter ke shirin maye gurbin ɗan wasan gabansu na ƙasar Albania Armando Broja, mai shekara 21, da ya ji rauni.
Everton na tsaye a kan babbar niyyarta ta sa hannu don ɗaukar ɗan wasan gaban Ajax Mohammed Kudus sakamakon bajintar da matashin mai shekara 22 ya yi wa ƙasarsa Ghana a Gasar cin Kofin Duniya.
West Ham sun haƙura, inda suka shiga neman sauran ‘yan bayan da suke da burin ɗauka bayan ta bayyana cewa ba za su iya shawo kan Middlesbrough har su sayar musu da ɗan wasan gefe na ƙasar Ingila, Isaiah Jones mai shekara 23 ba.
An ba da rahoton cewa Sevilla ta sa farashin fam miliyan 26 kan golanta ɗan shekara 31, Yassine Bounou bayan ƙwazon da ya yi a Gasar cin Kofin Duniya lokacin da ƙasarsa Moroko ta buga wasan kusa da na ƙarshe.
Sakamakon gagarumin goyon bayan da Uefa da Fifa suke samu a ƙoƙarinsu na ganin ba a ƙirƙiro wata Gasar Zaƙaƙurai ta Turai wato European Super League ba, masu yiwuwar zuba jari a Liverpool sun daɗa samun ƙwarin gwiwa, kuma har kuɗin sayen kulob ya ƙara tashi.