
Manchester United na shirin yin bincike don jin ko akwai yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaban Portugal da ke bugawa Benfica Goncalo Ramos, mai shekara 21, ko da yake, an faɗa wa kocinsu Erik ten Hag cewa ba lallai ne a samu zuwan wani ɗan wasan gaba a watan Janairu ba.
Chelsea ba sa fatan gaggauta shirinsu na ɗauko ɗan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 25, daga RB Leipzig a lokacin zafi da ke tafe, duk da raunin da ɗan wasansu na ƙasar Albania Armando Broja, ɗan shekara 21 ya ji.
Akwai “ƙwaƙƙwarar yiwuwar” ɗan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 22, zai bar Juventus a 2023, kuma ba a kau da yiwuwar fitar sa daga kulob ɗin ba a watan Janairu. Chelsea na cikin ƙungiyoyin da ke tuntuɓar ejan ɗinsa.
Chelsea na rige-rige da Manchester United da Liverpool kan ɗan wasan Borussia Dortmund Youssoufa Moukoko, amma duk kulob ɗin da ke da sha’awa sai ya tabbatar wa ɗan wasan gaban na Jamus mai shekara 18, cewa ba za a ɗauke shi don ya yi zaman benci ba.
Borussia Dortmund na fatan dangantakar Moukoko da koci Edin Terzic za ta taimaka wajen shawo kan ɗan gaban, wanda kwanturaginsa za ta ƙare a lokacin zafi mai zuwa, don ya yarda ya sa hannu a wata sabuwar kwanturagi a Disamba yayin da ƙungiyoyin Ingila da na Sifaniya ke shirin yunƙurawa kansa idan aka buɗe damar ɗaukar ‘yan wasa.
Real Madrid na sha’awar sa hannu da ɗan gaban Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 23, daga PSV Eindhoven saboda ya maye gurbin ɗan wasan gabanta na ƙasar Faransa Karim Benzema, 34.
Leicester na iya biyan har yuro miliyan 45 don ɗaukar Azzedine Ounahi daga Angers, ko da yake Barcelona ma na zuba ido kan ɗan tsakiyar Morokon mai shekara 22.
An ba da tayin ɗan gaban Portugal Joao Felix mai shekara 23, ga ƙungiyoyin Gasar Firimiya daidai lokacin da yake neman barin Atletico Madrid a Janairu, ana kuma ganin Manchester City da Manchester United da Arsenal sai Aston Villa a matsayin ƙungiyoyin da yake da yiwuwar zuwa. (Mail)
Ga dukkan alamu Manchester United da Arsenal ne zaɓin da Felix ke da shi, inda Atletico ke son jin tayi na sama da yuro miliyan 100 kan ɗan wasan.
An yi wa kocin Manchester United Erik ten Hag alƙawarin samun maƙudan kuɗi don ya sake gina ‘yan wasansa – duk da niyyar iyalan Glazer na sayar da kulob ɗin.
Manchester United na yunƙuri don ɗaukar ɗan bayan Netherlands Denzel Dumfries, mai shekara 26 daga Inter Milan, wadda za ta iya ba da dama ga Barcelona don ita kuma ta ɗauko ɗan wasan bayan United na ƙasar Portugal Diogo Dalot mai shekara 23.
Ɗan wasan da Liverpool ke hari Enzo Fernandez mai shekara 21, ba zai bar Benfica ba har sai mai buƙata ya ajiye yuro miliyan 120 kan ɗan wasan tsakiyar na Argentina.
Fulham na son ɗaukar ɗan bayan Arsenal na ƙasar Portugal Cedric Soares mai shekara 31 a watan Janairu.
Arsenal za ta yi yunƙurin sa hannu kan Youri Tielemans na Leicester City a Janairu, kuma an yi imani mai yiwuwa ne irin wannan mataki a lokacin zafi, idan ɗan wasan mai shekara 25 daga Belgium ya kammala kwanturaginsa.
Ajax sun amince su bar ɗan bayan Netherlands Daley Blind mai shekara 32, ya tafi a matsayin aro a watan Janairu.
Ɗan wasan gefen Ingila Samuel Iling-Junior mai shekara 19, ya yarda ya sa hannu kan wata kwanturagi ta tsawon shekara huɗu da za ta ba shi damar ci gaba da zama a Juventus, yayin da kwangilarsa ta yanzu ke shirin ƙarewa a lokacin zafi.
Barcelona na sha’awar ɗauko ɗan tsakiyar Boca Juniors na ƙasar Argentina Alan Varela, amma Ajax da Benfica sun fara tattaunawa don sa hannu kan ɗan wasan mai shekara 21, wanda kulob zai iya samu idan ya ajiye yuro miliyan 15.
Bayern Munich na tattaunawa don golan ƙasar Jamus Alexander Nubel mai shekara 26 ya koma kulob ɗin kafin ƙarewar zaman aro da ya je Monaco, maimakon ɗaukar wani sabon gola da zai maye gurbin Manuel Neuer da ya samu rauni.
Jefferson Lerma ya ƙi yarda da tayi birjik da aka yi masa a Bournemouth don haka ɗan wasan tsakiyar na ƙasar Kolombiya mai shekara 28, zai iya tafiya aro idan kwanturaginsa ta ƙare a lokacin zafi mai zuwa.