
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na na kokarin dauko mai kai hari na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 25, daga kungiyar Roma ta Italiya. (Caught Offside via Manchester Evening News)
Chelsea ta shirya domin shiga zawarcin dan wasan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund kan farashin fam miliyan 100, duk da ta kashe fam miliyan 600 lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa. (Telegraph – subscription required)
Ana sa ran Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani, zai taya kungiyar Manchester United kan farashin fam biliyan 4 a ranar Juma’a mai zuwa kamar yadda aka tsara. (Guardian)
Leicester ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Ingila James Maddison, mai shekara 26, a daidai lokacin da kwantiragin mai kai harin na Ingila ke karewa nan da shekara guda mai zuwa. (Telegraph – subscription required)
Dan wasan gaba na Sifaniya Ansu Fati, mai shekara 20, baya shirin barin kungiyar Barcelona, duk da tayin da kungiyar Tottenham ta yi masa, su ma kungiyoyin Arsenal da Bayern Munich, da Manchester United na zawarcin dan wasan. (Mundo Deportivo)
Nan da lokacin bazara ake sa ran Tottenham za ta dauko dan wasan Sevilla, kuma mai tsaron ragar Moroccan, Yassine Bounou, mai shekara 31 da ya yi fice a Bono, a daidai lokacin da suke neman wanda zai maye gurbin mai tsaron ragarsu ta Faransa Hugo Lloris ami shekara 34. (AS – in Spanish)
Ana sa ran Aston Villa za su yi tayin dauko zakaran gasar kwallon kafa dan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 30, sun shirya daukar dan wasan a karshen kakar nan, ko da ya ke ba bu wata damuwa tattare da sai da dan wasan tun da kwantiragin dan wasan ba zai kare ba sai 2027. (Mail)
Athletico Paranaense sun ki amincewa da tayin Barcelona da wasu kungiyoyi biyu kan matashin mai kai hari na Brazil mai shekara 17 Vitor Roque, wanda rahotanni ke cewa kungiyar Arsenal na zawarcinsa. (Goal via Globo Esporte)