
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta fita daga ‘yan hudun farko a teburin gasar Premier League, bayan kammala karawar mako na 29.
Tun a ranar Asabar Newcastle ta karbe mataki na ukun, bayan da ta ci United 2-0 a St James Park a babbar gasar tamaula ta Ingila, United ta koma ta hudu.
Ranar Litinin Tottenham ta je ta tashi 1-1 da Everton a Goodison Park a wasan mako na 29, inda Tottenham ta koma ta hudu, United ta yi kasa zuwa ta biyar.
Gurbi na biyar na masu buga Europa League ne, yayin da matakin farko zuwa na hudu ke wakiltar Ingila a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
To sai dai Newcastle da Tottenham da Manchester United, kowacce tana da maki 50 a teburin Premier League.
Newcastle ta koma ta uku, bayan da ta ci kwallo 41 aka zura mata 19 a raga tana da rarar 22, ita kuwa Tottenham ta ci 53, sannan 41 suka shiga ragarta tana da rarar 12, United kuwa 41 ta ci sannan 37 suka shiga ragarta.
Newcastle da Manchester suna da kwantan wasa bibiyu, ita kuwa Tottenham ta buga 29 kawo yanzu.
Arsenal ce ke jan ragama mai mai maki 72, sai Manchester City mai rike da kofin bara da maki 64, wato da tazarar maki takwas, saura wasa tara a kammala gasar bana.
United wadda ta lashe Carabao Cup a bana ta kai quarter finals a Europa League, wadda za ta fuskanci Sevilla gida da waje a watan Afirilu.
Kungiyar Old Trafford ta kai daf da karshe a FA Cup za ta fusakanci Brighton ranar 23 ga watan Afirilu a Wembley.
Ranar Laraba 5 ga watan Afirilu, United za ta karbi bakuncin Brentford a kwantan wasan Premier a Old Trafford.
Ranar 13 ga watan Agusta, Brentford ta doke United 4-0 a wasa na biyu da Erik ten Hag ya fara jan ragamar kungiyar Old Trafford a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.