Man United ta ziyarci Forest a Carabao Cup ranar LarabaCarabao Cup

Nottingham Forest za ta karbi bakuncin Manchester United a Carabao Cup zagayen daf da karshe da za su kara a City Ground ranar Laraba.

Kungiyoyin biyu sun fafata ranar 27 ga watan Disambar 2022 a gasar Premier League, inda United ta ci 3-0 a Old Trafford.

Wannan shi ne wasa na hudu da za su fuskanci juna a League Cup, inda United ta yi nasara a karawa uku baya.

United wadda ita kadai ce a Ingila ke buga League Cup da FA da Premier League da Europa League kawo yanzu na fatan daukar kofi ko kofuna a bana a karon farko.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like