
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na shirin sayar da kyaftin, Harry Maguire, mai shekara 30, da mai tsaron baya, Victor Lindelof, mai shekara 28 a karshen kakar nan. (Football Insider)
Aston Villa na duba yadda za ta dauki dan kwallon tawagar Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 29, wand ke buga wasannin aro a Inter Milan daga Chelsea. (Todo Fichajes – in Spanish)
Koci, Jurgen Klopp na son Liverpool ta bai James Milner, mai shekara 37 kunshin sabuwar yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar. (Football Insider)
Chelsea na son yin zawarcin golan tawagar Kamru, mai wasa a Inter Milan Andre Onana, mai shekara 26 a karshen kakar nan (InterLive, via Fichajes – in Spanish)
Chelsea da Newcastle ana bibiyar tsohon dan kwallon Manchester City, Brahim Diaz. Mai shekara 23 dan kasar Sifaniya na taka leda aro a AC Milan daga Real Madrid amma za a iya daukarsa a karshen kakar nan. (Sun)
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na fatan daukar dan kasar Faransa mai wasa a Galatasaray, Sacha Boey, mai shekara 22. (Aksam – in Turkish)
Marco Reus, mai shekara 33 na son ci gaba da taka leda har lokacin da zai yi ritaya a Borussia Dortmund, kungiyar da yake yi wa kyaftin yanzu haka. (Sky Germany – in German)
Tottenham za ta koma zawarcin dan kwallon Napoli, Kim Min-jae, mai shekara 26 a karshen kakar nan. (Football Insider)
Everton za ta dauki dan kwallon Jamaica mai wasa a West Ham, Michail Antonio, mai shekara 32 a bana, idan ta ci gaba da zama a Premier League. (Sun)
Dan kwallon tawagar Ghana, Mohammed Kudus, mai shekara 22 na fatan ci gaba da wasa a Ajax, duk da cewar Manchester United da Arsenal da kuma Liverpool na son yin zawarcin dan kwallon. (De Telegraaf, via 90min)
Besiktas na son biyan kunshin kwantiragin dan kwallon Congo mai wasa a West Ham, Arthur Masuaku, mai shekara 29. (Fanatik, via Inside Futbol)
Tsohon kociyan Everton, Frank Lampard na daf da komawa horar da tamaula, bayan wata biyu rabonsa da aiki, bayan da aka sallameshi a Goodison Park. (Sun)