Man Utd na son Ferguson, Man City za ta karawa Haaland albashiferguson

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na kwadayin cimma yarjejeniya da dan wasan Brighton asalin Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 18. (Football Insider)

United ta kuma sake mayar da hankali kan duba yada za ta daidaita da dan wasan Netherlands Rasmus Hojlund, mai shekara 20, da ke wasa a Atalanta. (Ekstra Bladet, via Sport Witness)

Manchester City ta shirya karawa Erling Haaland mai shekara 22 albashi a sabon kwantiragi kan fam dubu 500 a kowanne mako, a kokarin datse kokarin Real Madrid na saye shi.(Sun)

Leeds United na son sake cimma yarjejeniya da dan wasan tsakiya a Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 27, duk da cewa a bara ya barta zuwa Manchester City. (Daily Star)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like