An mana korar kare inji ma’aikatan MTN


 

 

 

Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya dakatar da daruruwan ma’aikata daga aiki a karshen wannan makon ba tare da biyansu wasu hakkoki nasu ba.

Da dama daga cikin wadanda aka kora daga aikin sun yiwa kafar yada labarai ta Premium Times dake a Najeriyan korafi kan yadda aka koresu ba kuma tare da biyansu wasu hakkokinsu da suka kunshi albashi da alawus ba.

Wasu daga cikin ma’aikatan da suka nemi a sakaya sunansu sunce babu takaimaimen takarda daga kamfanin dake a matsayin sheda na korar sai dai sun zo aiki ne kwatsam aka hana su shiga Ofis.

Tun bayan da hukumar da ke sanya ido a kan kamfanonin sadarwa, NCC a Najeriya ta ci tarar kamfanin dala biliyan biyar saboda alifin kin rufe layukan mutanen da ba su yi rijista ba har cikar wa’adin da aka diba ya wuce MTN ke fama da matsaloli.

You may also like