Manchester City ta lashe kofin gasar Firemiyar kasar Ingila


Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lashe gasar kofin Firemiyar ta kasar Ingila.

Kungiyar ta samu nasarar lashe gasar bayan da kulob din Manchester United ya yi rashin nasara a hannun kulob din West Bromwich Albion da ci 1:0 .

Kwallon da Jay Rodriguez ya zura a ragar kungiyar Manchester a filin wasa na Old Trafford ita ta saka kofin gasar ta Firemiya zai koma daya bangaren na birnin wato hannun kungiyar Manchester City.

Rashin nasarar da Manchester United ta yi yasa yanzu kulob din Manchester City ke saman teburi da maki 16 tsakaninta da kungiyar United dake biye mata.

Yanzu dai wasanni biyar ya rage a kammala gasar hakan na nufin koda Manchester ta ci dukkanin wasanninta biyar ba za ta iya kaiwa ga samun lashe gasar ba.

You may also like