Manchester United Ta Lashi Takobi Akan Pogba


 

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, na dab da sayen dan wasan kwallon kafar nan wanda yake taka leda a Juventus, Paul Pogba, akan kudi Euro miliyan 125, kimanin dalar Amurka miliyan 138,na tsawon shekar biyar inda ake sa tsamanin dan wasan zai dauki kudi Euro miliyan 12, a kowace shekara.

Pogba, na iya zama dan wasan da yafi kowane dan wasa tsada a nahiyar a bana, Pogba, dai ya bar kungiyar Manchester United, a shekarar 2012, a matsayin kyauta zuwa kungiyar Juventus.

Manchester United, dai ta nuna karara cewa lallai tana bukatar Paul Pogba, ya dawo kungiyar domin ya murza mata leda ganin cewa har yanzu akwai sauran kusa makoni hudu kafin a fara gasar frimiya na shekarar 2016-2017.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like