Mane da Sane sun bai wa hammata iska bayan wasan Man City



Sadio Mane Leroy Sane

Asalin hoton, Getty Images

Sadio Mane da Leroy Sane sun yi fada a dakin hutun ‘yan wasa, bayan tashi daga Champions League, kamar yadda wasu jaridu suka wallafa ranar Laraba .

Manchester City ce ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko zagayen quarter finals a gasar zakarun Turai.

Kamar yadda Bild da Sky da wasu jaridun Jamus suka wallafa, ‘yan wasan biyu sun bai wa hammata iska, bayan tashi daga karawar har sai da aka shiga tsakaninsu.

Bild cewa ta yi Mane ya naushi Sane tsohon dan kwallon City a fuska, har lebensa ya dan tsage.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like