Maniyyatan Aikin Hajin Bana Sunyi Zanga-zangar Lumana A Jihar NejaDaruruwan maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Niger sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin rai akan yadda suka ce sun share kwanaki suna zaune a sansanin Alhazai ba tare da an kwashe su zuwa kasa mai tsarki ba. 
Daruruwan maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Niger sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin rai akan yadda suka ce sun share kwanaki suna zaune a sansanin Alhazai ba tare da an yi jigilarsu zuwa kasa mi tsarki ba.

Maniyattan wadanda akasarinsu sun fito ne daga yankunan karkarar jihar, sun sheda cewa suna cikin wani yanayin na rashin sanin tabbas game da tafiyar tasu. Wasu daga cikin su, sunce sun share sama da kwanaki goma a sansanin Alhazai ba tare da an baiyana musu matsayin su gamaeda da tafiyar ba.

To amma jami’ar watsa labarai a hukumar Alhazai, Malama Hassana Isa Wushishi ta baiyana dalilin samun jinkirin. Tace saboda lamuran tsaro dake jihar Borno, shi ya sa aka karkata ko kuma aka fi maida hankali wajen kwashe maniyatta aikin hajji daga yankin. Dalili ke nan da aka samu tsaiko a cewar Malama Hassana.

Kawo yanzu dai kusan dukkan manyan jami’an hukumar Alhazai sunyi batan dabo daga sansanin Alhazan. To amma shugaban kwamiti mai kula da harkokin aikin hajji a Majalisar wakilan jihar, Salihu Mohammed yace manyan jami’an hukumar sun boye ne, domin kada maniyattan da suka fusata su huce haushinsi akan jami’an

You may also like