Manufar Sake Bullar Jita-Jitar Mutuwar Buhari – Fadar Shugaban KasaFadar Shugaban Kasa ta yi raddi kan sake bullar jita jitar mutuwar Shugaban Kasa, Muhammad Buhari inda ta bayyana cewa manufar masu yayata jita jitar ita ce na janyo rudani a cikin kasa.

Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya nemi al’ummar Nijeriya kan su yi watsi da wannan sabuwar jita jitar inda ya jaddada cewa babu wani abu da ya sami Shugaban. Ana dai ci gaba da yayata mutuwar Buhari a kafafen sanarwar na zamani.

You may also like