Manya manyan jami’am ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka kimani 900 suka nuna rashin amincewarsu da umurnin shugaban kasar na hana musulmi daga kasashen musulmi 7 shiga kasar Amurka.
Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran daga birnin Washington ta bayyana cewa wasika da ke dauke da sanya hannun wadan nan manya manyan jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya isa fadar shugaban kasa, sannan kakakin fadar white hause Sean Spicer ya tabbatar da cewa sakon ya isa hannun shugaban kasa amma shugaban ya kunnen wadannan manya manyan jami’an diblimasiyya kan ko su aiwatar da umurnin shugaban kasa ko kuma su bar ayyukansu.
A dayan bangaren kuma alkalin alkalan birnin Washintone Karl Racine ya bayyana cewa dokar shugaban kasa kan hana mutane daga wasu kasashe musulmi da ya ambata ba abin aiwatarwa bane. Racine ya kara da cewa dokar ta sabawa dokokin kundin tsaron mulkin kasar wanda ya bukaci daidatawa tsakanin Amurkawa maza da mata mazauna cikin kasar ko kuma wadanda suka shigo kasar bisa ka’ida.