Manya-Manyan Kura-kuran Shugaba Buhari Guda 15.



Matukar ba a dauki matakin gaggawa ba, Buhari zai zama shugaban kasa na farko da zai rasa tikitin takarar jam’iyyar sa a za6en cikin gida.

Buhari da na sani kafin za6e ba shine ainihin Buhari yanzu a matsayin shugaban kasa ba. Buhari da na yi wa yakin neman za6e tsayayye ne, jajirtacce kuma kaifi daya. Aisha Buhari ta yamutsa hazo da tattaunawa da ta yi da BBC,  sai dai abinda ta fada ya gasgata abinda na sha fada akan Mijinta. Matukar ya tabbata tawagar su Mamman Daura ne ke juya akalar wannan kasa, shakka babu akwai rashin gogewa, kasancewar yawancin su gogaggu ne a fannin matslolantaka da satar fasaha.

1. Tawagar sun jefa kasa da kuma shugaban kasa cikin yanayin kwatance, tare da jagorantar tattalin arziki zuwa kwazazzabon durkushewa, darajar kudinmu ya zazzaye zuwa magaryar tukewa, tare da dagawa shafaffu da mai kafa suna cin karensu ba babbaka. Sun yi wa gawurtacciyar Jam’iyyar da bangarorin kasar nan suka gina kamshin mutuwa.

2. Kusan kullum raina kan sosu, yadda na ga an mayar da shugaban kasar mu kamar wani dan wasan kwaikwiyo da wasu ‘yan gambara da suke yawan cilla kafafuwansa zuwa kasashen Ketare, suke kuma lankwasa hannuwansa ga kin hukunta masu kashi a gindi, sannan suke murguda bankinsa ga suburbuda katobara.

3. Tun daga zubin Ministoci har zuwa hukumomin gwamnati, an yi za6in tumun dare, kamar yadda aka za6i lusarai cikin ‘yan tawagar shugaban kasa, tun daga farkon kamun ludayin gwamnatin. Kazalika haka wannan Makauniyar tawaga ta bayar da gurguwar shawarar bayar da mukamai ga Fitattun ‘yan jari hujjar jihar Kaduna, wadanda da dama daga cikin su gwauron gwamnatin baya ne, ko kuma wadanda a fili suka yi wa PDP yakin neman za6e.

4.  Guda daga cikin ‘yan tawagar, wanda ya na daga kusoshin gwamnatin, shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, gwamnatin Jonathan ta bashi mukami a kwamitin kar-ta-kwana na harajin man fetur a 2012. Wannan ya sa yayi fatali da tayin mukamin da Buhari yayi masa na Sakataren yakin neman zaben Jam’iyyar CPC, saboda ya hango Buhari ba lallai ya kai labari ba.

5.  Mu dauki misalin nadin Ministan jihar Sokoto. Duk wani dan APC Na halak ba zai yi farin ciki da nadin diyar dan jari-hujjan jihar Kaduna Alhaji Abubakar Alhaji, Aisha Abubakar da aka nada a matsayin Minista daga jihar Sokoto ba. Kiri-kiri Aisha ta yiwa Gwamnan jihar Sokoto yakin neman za6e a Jam’iyyar PDP tare da dan uwanta Aminu Abubakar Alhaji wanda yayi takarar dan majalisar wakilai na daga kananan hukumomin Tambuwal/Kebbe.

6.  Kazalika babu dan Jam’iyyar APC na amana da zai yi farin ciki da zabin Zainab Shamsuna Ahmed diyar dan jaridu -hujjar jihar Kaduna Yahaya Hamza, a matsayin Minista daga jihar, wacce Zainab ita ce ta shugabanci NEITI a zamanin mulkin Jonathan sannan kuma ta ba W wa PDP gudunmawa yayin yakin neman za6e.

7.  Duk wani mai shaidar katin Jam’iyyar APC ya ji bakin ciki da ya ga Mohammed Bello,  da ga Musa Bello, wanda abokin Mamman Daura ne, a matsayin Minista daga jihar Adamawa. Mohammed Bello shine ya jagoranci hukumar Alhazai ta kasa lokacin Jonathan, amma an ba shi matsayi a Birnin Tarayya. Na tabbatar da ya yi wa Jonathan tutsu, da ana faduwa za6e zai sauke shi daga mukamin sa.

8.  Dubi yadda ‘yan tawagar suka cillar da halastaccen dan Jam’iyyar APC a jihar Enugu kamar Osita Okechukwu suka nada Geoffrey Enyeama, wanda bai taba ganin Buhari ba, bai kuma taba tsinanawa Jam’iyyar APC Komai ba amma an ba shi ministan harkokin kasashen Ketare.

9.  Ko akwai wani dan siyasar APC da zai yi farin ciki da Sanata Ita Enang wanda ya jagoranci tallan takarar Jonathan amma ya samu mukamin babban mai ba wa shugaban kasa shawara akan majalisar dattawa. Ko Sanata Victor Ndoma-Egba, wanda shima ya jagoranci tallan takarar Jonathan amma an ba shi matsayin shugaban raya Yankin Neja Delta. Yayin da halastaccen dan Jam’iyyar APC kamar Sanata Magnus Abe aka cilla shi a kwandon shara. Wanda har ‘yan sanda sai da suka harbe shi a yayin yakin neman zaben jihar Ribas.

10.  Aisha Buhari da ta yi mamaki ina halastattun Jagororin tallata takarar Buhari kamar irin Sanata Olorunnimbe Mamora, Faruq Adamu Aliyu, Dele Alake, Barista Ismail Ahmed, Architect Waziri Bulama, Yusuf Tuga, Yakubu Lame, Dr. Hassan Lawan, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, Umaru Dembo, Ubale Hashim, Umar Dangiwa, Ibrahim Hussein Abdulkarim da sauran su?

11. Dole zuciyar Aisha Buhari da sauran magoya bayan Jam’iyyar APC ta sosu domin ganin yaran Jonathan na rike madafun iko a wannan gwamnatin. Ya kamata Wadannan ‘yan tawagar su sani cewa, hukumomi 12 na gwamnatin Tarayya har yanzu yaran Jonathan ne ke rike da su, kazalika Minista Injiniya Sulaiman Adamu an nada shine ba don gudunmawar sa ga nasarar Buhari ba sai don ya kasance dan dangi ne.

12. Ku duba yadda aka kara nada Manajan Daraktan Umaru Ibrahim NDIC. Jonathan ne ya nada Ibrahim a watan Disamba 2010 amma Buhari ya kara nada shi domin ya yi shekara biyar, kamar babu wanda ya cancanci wannan matsayin a kafatanin Jam’iyyar APC. Haka kowa zai yi mamakin me ya sa Darakta Janar ta PenCom, Mrs Chinelo Anohu-Amazu, har yanzu ta na wannan matsayi, bayan ya tabbata nadin ta ya saba da tanadin dokar kasa. Shin Buhari yana tunanin Jam’iyyar sa na farin ciki cewa, Malam Sani Sidi, na hannun damar tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, har yanzu shine shugaban Hukumar agajin gaggawa ta NEMA?

13.  Duk wanda ke yi wa Buhari da Jam’iyyar APC fatan alheri dole wannan abu ya sosa masa zuciya. A matsayin ta na matarsa wacce ta mara masa baya yayin yakin neman zaben, Aisha Buhari ta na da hurumin yin korafi yayin da wasu ‘yan baranda suka hana gwamnati rawar gaban hatsi kuma al’amura suka damalmale a Jam’iyya. Ba tabbatar har yanzu tana son Mijinta fiye da fiye da wadanda suke sukar ta ko ganin ba ta kyauta ba. Har yanzu ita ce mafi kusanci da shi a zahiri da badini.

14. Ga masu yi wa Buhari Makauniyar soyayya, su sani cewa a bisa doron bayan Jam’iyyar APC ya taka zuwa matsayin shugaban kasa. Karkashin Jam’iyyar ya fara dusashewa, halastattun ‘yan Jam’iyyar da suka taka Muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya zama dan takara an yi watsi da su. Yayin da ‘yan cin moriyar ganga suka zama masu fada aji. Jam’iyyar APC na fama da matsanancin Zazzafan zazzabi, wacce ta ke bukatar allurar da za ta warkar da ita.

15. Akwai tikekiyar damuwa dangane da yanayin siyasar Buhari da kuma Jam’iyyar APC. A halin da yau ta ke ciki, idan ba mu’ujiza za ta yi ba, Buhari zai zama shugaban kasa mai ci na farko da zai rasa tikitin takara a zaben fitar da dan takarar Jam’iyyar sa. Ko kuma ya zama shugaban kasa na biyu a tarihin siyasar Nijeriya da zai sha kaye yana kan karagar mulki.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like