Manyan Alkawuran ‘Yan Siyasa A Zaben 2023 Mai ZuwaDuk da za a ce ba irin alkwarin da ba a taba ji ba a baya, wannan karon wasu ‘yan takarar na takatsantsan da kalaman da su ke furtawa.

Daga yanda kamfen din ya ke tafiya a fili ya ke, ba lalle a tsakanin jam’iyyu biyu kamar yanda a ka saba a ke fafatawa ba, don akalla akwai jam’iyyu 4 masu tasiri da za a shata daga da su a zaben.

Ganin irin alkawuran da a ka saba yi, dan takarar gwamna na APC a Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ba zai tona wa kansa rami ta hanyar daukar alkawuran da ba zai iya ba.

Nasiru Gawuna

Nasiru Gawuna

Gawuna na magana ne a wani taron masu ruwa da tsaki na siyasar Kano a Abuja.

Shi kuma dan takarar jam’iyyar AA a Yobe Muhammad Bello Arabi ya ce su na alfahari da shaharar dan takararsu na shugaban kasa Manjo Hamza Almustapha da in sun yi alwashi kan inganta tsaro ba za a ce zane kan ruwa su ke yi ba.

Hamza Al-Mustapha

Hamza Al-Mustapha

Magoya bayan ‘yan takara irin su Jauro Hammadu Saleh na cewa ko rantsewa zai iya yi cewa Rabi’u Kwankwaso na NNPP zai cika alkwari in an ba shi dama.

Ita kuma Maryam Shetty da ke matsayin ‘yar gani kashenin APC ta ce dan takarar su Tinubu ya cika alkwari a baya ma balle yanzu da ya ke takarar shugaban kasa.

Maryam Shettima

Maryam Shettima

Haka dai ‘yan takara da magoya bayansu ke magana kan zaben da za a yi shi a karo na farko tun 2003 ba shugaba Buhari a jerin ‘yan takara.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like