Manyan dillalan mai sun tabbatar da samun mai daga NNPC


Manyan dillalan man fetur da kuma ya’yan kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta IPMAN a ranar Talata sun tabbatar da samun mai daga kamfanin mai na ƙasa NNPC.

A cewar sakataren kungiyar manyan dillalan mai ta MOMAN, Obafemi Olawore yace ya’yan kungiyar sun fara samun man fetur din a ranar Litinin.

Lawore yace duk da cewa kason da suke samu daga NNPC bai kai wanda suka yi tsammani ba amma sun dawo da rarraba man a wurarensu dake faɗin kasarnan.

Ita ma kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta IPMAN na cewa wuraren a jiye mai na Ejigbo da kuma Mosimi waɗanda ke da muhimmancin gaske wajen raba mai a yankin kudu maso yamma sun samu mai wadatacce inda suka yi alkawarin cewa karancin mai da ake samu a Lagos da Ogun zai kawo karshe a kwanaki kaɗan masu zuwa.

A cewar shugaban kungiyar ta IPMAN a jihar Lagos, Alhaji Alanamu Balogun kafin fara wahalar man, NNPC na basu motocin mai shida a kowacce rana amma daga kwanaki biyar da suka wuce kamfanin na basu mota 80 a kowacce rana.

Kungiyar tace NNPC ya cika alkawarin da yayi na samar musu daman.

You may also like