Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya amince da takardar yin ritaya da Shugaban Hafsoshin Nijeriya, Janar Gabriel Olonisakin da kuma Shugaban rundunar Sojan Ruwa, Vice admiral Ibok- Ete Ekwe Ibas suka mika masa.
Tuni dai Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali ya nemi manyan hafsoshin kan su mika ragamar iko ga wadanda ke bin su a mukami wanda kuma ake sa ran Shugaban Rundunar Sojan Sama, Air Marshal Abubakar Sadik ne zai maye gurbin Shugaban hafsoshin Nijeriya a matsayin na riko kafin Shugaba Buhari ya yi sabon nadi.