
Asalin hoton, OTHER
Rahotanni sun nuna cewa ana takarar tsakanin Liverpool da PSG da Manchester City da kuma Real Madrid kan son saye dan wasan tsakiyar Ingila, Jude Bellingham.
Bellingham na wasa ne a Borrussia Dortmund da ke Jamus, kuma yana da kwantiragi har sai 2025.
Matashin dan wasan na daga cikin wadanda suka haska sosai a gasar kofin duniya da aka kammala a Qatar, kuma ana sa ran duk kungiyar da za ta saye shi daga cikin manyan kungiyoyin, ba zata biya kasa da fam miliyan 100 ba.
Dama Liverpool ta dade tana sa ido kan dan wasan, kuma shigowar Manchester City da kuma darajar gasar Premier League, na nufin akwai yiwuwar Bellingham ya je Ingila.
Faransa ce ta cire Ingila a zagayen quarter-finals na Qatar 2022, to amma Bellingham ya nuna irin tasirin da ya ke da shi ga tawagar Three Lions, duk da shekarunsa 19.
Matashin ya kafa tarihin zama dan wasan Ingila mafi karancin shekaru da ya ci mata kwallo a gasar kofin duniya, tun bayan Micheal Owen.
Bellingham ya ci kwallonsa a wasan da Ingila ta doke Iran a gasar Qatar 2022.
Kwanaki kadan suka rage a bude kasuwar cinikin yan wasa ta watan Janairun 2023.