Shugaban Jam’iyyar masu ra’ayin kawo sauyi a haramtacciyar kasar Isra’ila ta Meretz ya bada labarin cewa: Manyan jami’an sojin Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila sun isa sansanin jiragen saman garin Tabuk na kasar Saudiyya domin tallafawa masarautar Ali-Sa’ud a yakin da ta kaddamar kan kasar Yamen.
Shugaban jam’iyyar masu rajin kawo sauyi a haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Meretz” Zehava Gal-On ya bayyana cewa: A halin yanzu haka manyan kwamandojin sojin Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila fiye da 120 suna sansanin jiragen saman sarki Faisal da ke garin Tabuk na kasar Saudiyya domin taimakawa masarautar Saudiyya a yakin da take yi a kasar Yamen.
Gal-On ya fayyace cewa: Tuni dama mahukuntan Saudiyya sun kulla yarjejeniya da Amurka kan girka na’urar kakkabo jiragen sama da makamai masu linzami a sansanin jiragen saman Sarki Faisal da ke garin Tabuka, don haka sojojin na Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka je domin sarrafa na’urorin tare da kula da su.
Tun a cikin watan Maris na shekara ta 2015 masarautar Saudiyya da hadin gwiwar kawayenta na kasashen Turai da Amurka gami da ‘yan koranta na kasashen Larabawa suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen, inda a halin yanzu suka kashe daruruwan mutane tare da jikkata wasu dubbai baya ga tilastawa dubban daruruwa yin gudun hijira.