Manyan Kwamandojin Sojin Nijeriya Za Su Yi Bikin Kirismeti A Fagagen Daga Da Ke Jihar Borno


 

 

Rundunar sojin Nijeriya ta umurci manyan kwamandojinta, su tafi jihar Borno domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti tare da dakarun su dake bakin daga.

Zalika rundunar, ta bayyana shirin bude wasu manyan hanyoyi da aka rufe a Jihar Barno saboda rikicin kungiyar Boko Haram.

A zantawarsa da sashin Hausa na RFI, daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman Kukasheka yace, a halin da ake ciki rundunar sojin Najeriya ta kafa sansanoni 14 a cikin dajin Sambisa.

Kukasheka ya ce babban dalilin bawa manyan kwamdojin soji umarnin gudanar da bikin Kirsimeti a Borno, shi ne don karawa sojin da ke bakin daga kwarin gwiwa.

A gefe guda kuma, darakatan yada labaran rundunar sojin ya ce, a wani yanayi da ke nuna ingantar tsaro a yankunan da a baya ke fama da hare haren Boko Haram, za’a bude manyan hanyoyi guda biyu da aka rufe saboda rashin tsaro.

Hanya ta farko it ace wadda ta tashi daga garin Maiduguri zuwa Damasak, sai kuma wadda ta tashi daga Maiduguri zuwa garin Baga.

You may also like